ILLOLIN WAYAR HANNU KA LAFIYAR JAMA'A

ILLAR WAYAR SALULA GUDA GOMA (10) GA LAFIYAR JIKI:

Wayar salula dai  wata abu ce da ake kiran ta da suna handset ko wayar hannu, ta kasance fasahar da aka samu a karni na 20. Wayar salula ta zamanto wata fasaha ce wadda  ta mamaye ko ina a cikin duniya, birane da  kuma kauyuka.

Masana kiwon lafiya sunyi bincike sosai su kace duk da amfanin da wayar salula ke da shi ga al’umma, har ila yau tana kuma dauke da wani abu wanda mai cutarwa ne ga rayuwarsu. da take iya yiwa lafiyar bil’adam.

Ga kadan daga cikin illolin wayar salula ga jikin Dan Adam:

1-Cancer: Masana kiwon lafiya sun bayyana cewar duk lokacin da mutun ke magana kimanin hyper-microwabes 9000khz na garzayawa kwakwalwar shi, wanda kuma shine ya kan haddasa illolin masu yawa da suka hada da kara yanayin da ita kwakwalwar da 1°C wanda kan iya haifar da cutar kansar kwakwalwa.

2- Sleep disorders: Wannan sanin kowa dadewa amfani da ita wayar salula da mukeyi ta hanyar chating ko kira yakan sa mu dade bamuyi bacci ba cikin dare yawaitar yin haka har ta sabawa Ζ™waΖ™walwar mu abin yazama jikin mu. wani bincike ya nuna awa 2 kafin baccin na kallon fiskar waya yana shafar bacci mai lafiya sannan yahana hutu mai dadi sakamon hasken wayar da kagama daukar lokaci kana kallo.

3- Increased accident-risk : Yana kara yawaitar hatsari, binciken hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta nuna cewa daga zuwan waya zuwa yanzu hatsari ya karu fiye da kashi 3 zuwa 4 kafin wayar salula tazo, yayin da mutum yake danne dannen wayar salula tana dauke masa hankali akan hanya, har yakai ga accident.

4- Obesity: Bincike ya nuna cewa Yana kawo matsanancin qiba mara amfani saboda karancin motsa jiki sakamakon yawan kwanciya ko zama ana  amfani da ita wayar kamar chatin.

5- Hearing impairment: kira a wayar salula samada awa daya (60 minutes) a kunne yana rage lafiyar ji. Yin waya yayinda take yin chaji yana kashe kunne gabadaya in andauki tsawon lokaci anayi.

6- Eye problems: Yana kawo matsalar ido, bincike ya nuna yawan dadewa ana amfani da ita wayar salula yana iya haddasa cutar ciwon ido, saboda haske da “screen” na wayar ke samarwa, ba wai ga ido kawai hasken na screen ya tsaya ba, yakan kai ga jijiyoyin ido daganan kuma sai ya rasa zuwa  cikin kawkwa.

7- Infertility: Rashin Haihuwa, bincike ya nuna Sinadarin radiation frequency dake fita daga wayar hannu ko komfuta musamman yawan saka wayar aljihun wando ko dora komfuta a kan cinyoyin kafa biyu yana kashe ko rage qarfin sinadaran haihuwar sperm.

8 - Infection: Wani bincike ya nuna wayar salula na dauke da Kwayoyin baktriya fiye da ban daki (toilet) sabida yawan gaisuwa da mutane sannan ka tana shi da hannun ka kafin ka wanke, wassu ma suna tabawa sannan kazo kaci abinci da hannun hakan nasa Kwayoyin cuta su samu hanyar shiga jiki.

9- Skin allergies: Wassu daga cikin wayar salula musamman bakckberry suna dauke da sinadaran nickel, chromium and cobalt wanda yakan kawo kaikayi da kurajen fata ga wassu mutanen.

10- Stress : Yawan damuwa, bincike ya nuna daukan lokoci ana amfani da wayar salula tana kawo chanza taswizar Kwakwalwa wanda hakan zai iya kawo stress.

Comments

Popular posts from this blog

Yadda zaka ida ceke bayanan ka na tsarin Nisal..

Ziyarar Mallam Dr. Dikko Umar Radda ga Bankin Raya Africa

RADDIN MURIC ZUWA GA BISHOP MATHEW HASSAN KUKAH!!!