Posts

Showing posts with the label Technology

Dalilin da yasa kasashen yamma suka fi mu cigaba a bangaran fasaha...

Image
Idan ka kwantar da ranka kayi tunani da kyau za ka fahimci cewa akwai wasu dalilai da yasa kimiyya da fasaha suka ci gaba a duniya musamman a Ζ™asashen yamma. Sai dai dalilan a bayyane suke kuma kusan kowa ya san su, abun nunawa guda a nan shi ne “menene madogarar cigaban bunΖ™asa ilimi da binciken kimiyya da fasaha” bayan kuma mutane ne masanansu. A yau duniyar kimiyya da fasaha sun yi ci-gaban da ya haura gaban mamaki domin wasu abubuwan da za ka ji ana samarwa da binciken da ake yi wajen gano wani abu dole sai dai kayi shiru don mamaki. Amma menene dalilin haka? A takaice kuma dalili guda daya shine “ bincike .” Da bincike ake juya duniya, da shi ake canja duniya kuma da shi ake bunkasa komai. Shekaru dari da suka wuce a baya babu ilimin yanar gizo, yau ga shi ta dalilinsa ka kan iya ganin mutumin da yake wata nahiyar kai tsaye, kawai taba jikinsa ne ba za ka iya ba. Shekaru dubu da suka wuce kafin ka kai wata kasa sai ka shafe tafiyar watanni, a yau za ka iya daga murya k