Ziyarar Mallam Dr. Dikko Umar Radda ga Bankin Raya Africa


 Gwamnan Jihar Katsina Ya Ziyarci Bankin raya Africa, Ya nemi tallafin su kan bunkasa harkar Noma, Ilimi da Lantarki.


Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, ya ziyarci Bankin Raya Afirka (AFDB) inda ya gana da Babban Daraktan Bankin, Mista Lamin Barrow a ofishin Bankin da ke Abuja a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuni 2023. Ziyarar na da nufin tattauna batun saka hannun jari da tallafin shiga tsakanin Katsina da Bankin don taimakawa wajen bunkasa samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al’ummar jihar Katsina.


Dr Radda, a cikin jawabin nasa, ya ce, "Muna bukatar taimakon Bankin musamman don magance gibin abubuwan more rayuwa na jihar, kamar wutar lantarki." Ya kuma kara da cewa, makamashin da ake sabuntawa ya kasance wani muhimmin ababen more rayuwa da ake bukata domin samun karuwar tattalin arziki a jihar, wanda hakan ya sanya ziyarar ta zama wajibi. Gwamnan ya kuma bukaci Bankin ya ba da goyon baya don bunkasa muhimman amfanin gona, da suka hada da auduga da ayyukan noma wadanda kuma za su samar da ayyukan yi ga matasa. Daga karshe ya mika godiyarsa ga shugabannin bankin da suka halarci taron tare da fatan samun kyakkyawar alaka da bankin nan ba da dadewa ba.


A nasa bangaren, Darakta Janar na ofishin Najeriya, rukunin bankin ci gaban Afirka,

Mista Lamin Barrow ya nuna jin dadinsa da ziyarar tare da yabawa manufar Gwamnan na kawo sauyi ga al’ummar jihar. Ya kuma ba da tabbacin goyon bayan bankin a bangarorin tattalin arziki da aka ambata.


A tare da gwamnan akwai shugaban ma'aikatan sa Alh. Jabiru Tsauri; Babban magatakardan gwamna, Alh. Abdullahi Turaji; Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan, Kaula Ibrahim; da kuma babban mataimaki na musamman ga gwamna kan kafafen sadarwa na zamani, Isah Miqdad da sauransu.


SSA Isah Miqdad

Comments

Popular posts from this blog

Yadda zaka ida ceke bayanan ka na tsarin Nisal..

Federal Government Re-open Survivalfund!!!