RADDIN MURIC ZUWA GA BISHOP MATHEW HASSAN KUKAH!!!


RADDIN MURIC ZUWA GA BISHOP MATHEW HASSAN KUKAH

RADDIN MURIC ZUWA GA BISHOP MATHEW HASSAN KUKAH

SAKO ZUWAGA BISHOP KUKAH DAGA MURIC:

Bishop din Diocese na Sokoto, Rev. Fr. Hasan Kukah, a maganar da yayi jiya ya ba da shawarar cewa ya kamata a yi juyin mulki da wani Dan Kudu ya mamaye kujerar mulkin Najeriya. Ya kuma ambaci Musulunci a matsayin addinin da yake kawo tashin hankali. Kungiyar kare hakkin bil adama ta musulinci ta Najeriya, kungiyar Rajin kare hakkin Musulmi (MURIC), ta bayyana bishop din a matsayin mai muguwar dabi’ar ci da ceto Kuma mai kawo hargitsi.

Wannan an bayyana wa manema labarai ne a wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, 27 ga watan Disamba, 2020 ta hannun Farfesa Ishaq Akintola, daraktan kungiyar.

Mun yi matukar mamakin wannan ta hanyar kai hare-haren da aka fara jiya wanda Rev. Hasan Kukah ya kaddamar kan Musulunci saboda tsana ta addini. Bishop din Katolika na Diocese na Sakkwato ya ambaci Musulunci a matsayin addini tashina-tashina. Ya kuma yi kira da a yi juyin mulki ga zababbiyar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ya zarga da nuna son kai.

A cewarsa Babu yadda za a yi wani Shugaban Kasa da ba Musulmi ba dan Arewa ya kwatanta wani abu kadan daga abin da Shugaba Buhari ya yi ta hanyar nuna son kai da kuma kau da kai ga wasu. Yace ya tabbata inda ba Buhari yake mulki ba, inda wani wanda ba Dan arewa ba ne ba kuma ba Musulmi ba da tuni anyi juyin mulki.

Wannan furcin na Bishop Kukah furuci ne wanda bayada wata hujja ko wani tsari saboda haka bazamu bari ya tafi hakanan ba babu wani kalubale ba. Maganar Kukah ta rashin tunani ce, maganace wacce yayi bai tsaya ya tauna ba. Wannan ita ce mafi munin zance, Managace ta sakarci da son rai. Itace magana mafi muni a wannan shekara ta 2020. Hasan Mathew Kukah mayaudari ne wanda yake sakin jikinsa cikin mutane kamar na kwarai. Kukah yana daukar matakin lalata duk wani shugaban da ya kasance Musulmi. Musamman, mun yi matukar bakin ciki da cewa irin wannan mummunan ra’ayi na son zuciya da bullowa da sabbin fitin-tinu yana zowa ne daga sakataren Kwamitin Zaman Lafiya na Najeriya. Halayyar sa bata dace da matsayinsa ba.

Kukah ya ambaci addinin Islama a matsayin addinin tashin hankali, amma kuma dan uwansa, Gana, ya kasance yana horar da ‘yan ta’adda tare da kashe Musulmi a Benue tsawon shekaru. Shin Kukah yana da cikakkiyar masaniya game da akidar wadanda ke tare hanya ga matafiya a yankin Filato, suna kashe duk Musulmin da ke cikinsu kuma suna jefar da su a cikin tafkuna da rijiyoyin da ke yankin Filato, shike nan ba za a sake ganinsu ba. Bamu taba yin wani abu ba saboda munsan akwai hukuma. Ta yaya wadanda ke ba da horo da kuma ba da makamai ga masu kisan gilla, wai su ne za su juya su kira Musulunci a matsayin addinin tashin hankali?

Bishop Kukah yana zaune ne a tsakiyar Birnin Musulunci kuma ba a taba kai masa hari ba. Kukah kuma ya san irin karimci da sadakokin da mutanen Sakkwato suka yi masa. Inda ka kasance mutun mai mayar da alheri. Ya kamata irin wannan zargin ya fito daga wani, daga wani waje kuma, Kukah ya ciji yatsa.

Amma ta yaya za ka zolayi Arewa? Shin bakwa daga cikin wannan yankin na arewa? Shin wannan mutumin ne da yake ce yana so ya ceci almajirai miliyan 10? Mun godewa Allah da muka dakatar da shirin naku na gina gidan wasan dabbobi. Kuna izgili ga Arewa amma kuna nuna kuna son ‘ceton’ yaran Arewa. Kun bayyana muna cikakken halin ku da abinda kuke nufi.

Mun fahimci sanadin bacin ran Kukah. Rashin samun wancan haraji a kan kowane kaya da aka shigo da su, gami da jiragen sama masu zaman kansu, yanzu babu su. Babu kuma kwangilar Biliyoyin kudi. Wannan shine dalilin da ya sa Kukah ya koma ci da ceto na nulli secundus.

Kukah ya kira ayi juyin mulki ne saboda baya samun ci-daceto a gwamanatin Buhari. Amma Shin Kukah yana sane da cewa wannan juyin mulkin zasuyi shi ne a coci? Amma Menene sakamakon irin wannan da ya faru a kasar? Ko da Nzeogwu zai juya cikin kabarinsa a daidai lokacin da ake yunkurin juyin mulki na muradan choci.

Bakuyi tunani ba ace anyi wannan shirin a dai dai bikin Kirsimeti lokacin da yakamata a samu kauna da soyayyar ku. ‘Yan Najeriya suna ganin abinda ke faruwa fa. Muna aika sakonnin nuna soyayya zuwaga Bishop Kukah a lokacin Kirsimeti. Ya amsa da fushi da raini da cike da kiyayya. Shin wannan ya dace?

Zargin da Kukah yake yiwa PMB na nuna sonkai wannan ba haka yake ba. Akan Nadin da Buhari ya yi kamar yadda wata jarida ta yanar gizo ta wallafa ya karyata batun magana ta Kukah. Binciken ya nuna cewa A nadin da Buhari yayi Arewa maso Yamma sun samu nade-nade 37, Arewa maso Gabas sun samu 29, Arewa ta Tsakiya ta samu 21, Kudu maso Yamma na da 63, Kudu maso Gabas ta samu 25 yayin da Kudu maso Kudu ta samu 24. Kudu maso Yamma sun fi amfana. Amma Buhari shi Bayarbe ne? Ya ba Kudu maso Yamma kusan ninki biyu na abin da ya ba nasa Arewa maso Yamma. Wannan son zuciya ne? Muna kalubalantar Kukah da ‘yan koren sa na karya su kawo nasu bayanan.

Wannan shi ne abibda ake fadi cewa Arewa gaba daya tayi babakere kuma a dalilin haka ne Kukah yake zargin Buhari da nuna son kai, ya samu mukamai 87 yayin da Kudu ta karbi 112. Kenan duk farfagandar karya da zargin nuna son kai ga Buhari sun fadi kasa warwas kamar fakitin kati, la’akari da wannan bincike. Zance Kukah zance ne kawai na rikicin addini bayada wani tushe ko mafari.

Ya ci gaba da tabbatar da cewa wannan mulkin mallaka na arewa, na Daular Usmaniyya, musulinci da fulaninci ba su wuce tatsuniya ba, da shaci fadi. Wakoki ne kawai wadanda ‘yan mamayar siyasa, ‘yan bautar kabilar su da masu bautar addini suka amince da su don yaudarar’ yan Najeriya.

Kukah yafi kowa sanin wadanda ke nuna son kai amma ya zabi zama mai son zuciya yana mayar da laifi inda bai kamta ba. Rev. Samson Olasupo Ayokunle, shugaban kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) da kanshi ya bayyana irin alfarma ta musamman da Cif Olusegun Obasanjo ya yiwa Kiristoci lokacin da yake shugaban kasa. An bayyana hakan ne a Cocin Baptist na Orita Mefa, Ibadan, a ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba, 2020 yayin hidimar jana’izar Fasto na wa’adi biyu na Obasanjo, Rev. S. T. Ola Akande.

Shugaban CAN ya zuba wa Obasanjo kundila saboda fifita Kiristoci a lokacin mulkin sa. Daga cikin ni’imomi na musamman Wadanda yayi musu wanda aka ambata sun hada da raba filaye ga ofishin Baptist a Kubwa, Abuja; sannan da wani kason fili ga Baptist a garin Festac, Legas; sannan kuma an bada wani cocin kason cocin da ke garin Satellite da kuma wani a highbrow Ikoyi, shi ma a cocin. Babu wani shugaban Musulmi ko kungiyar Musulunci da ta zargi Obasanjo da nuna fifiko har zuwa yau. Watakila Kukah yana tsammanin Allah yana barci a lokacin mulkin Obasanjo. Amma babban bishop din yanzu yana da karfin da zai tunatar da ‘yan Najeriya cewa Allah baya bacci.

Don haka suna son a sauya gwamnati da karfi. Amma maimakon jira har lokacin zabe na gaba saboda dimokiradiyya, sai suka zabi sauyi da karfi. Amma #EndSARS sun gaza. Dole ne su fadi bakaken maganganu ga shugaban kasa.

Bayanin Kukah game da juyin mulki shir me ne yazama kamar shaidan. Muna sane da cewa fararen hula ko yaushe suna tunkarar juyin mulki. Don haka sha’awar Kukah ba sabon abu bane. Amma me yasa Kukah ke tunzura mutane? Ku ci gaba da shirya juyin mulki Kukah, Wa ya sani? Ko kai ke neman mataimakin shugaban kasa. Kuna nan kuna gwagwarmaya. Gamu gani

Farfesa Ishaq Akintola, ✍️ Munir Assalafiy
Darakta, MURIC


@HASSAN ABUBAKAR MUSA0 9038702411 hassanabubakarmusa081@gmail.com                                  

Comments

Popular posts from this blog

Yadda zaka ida ceke bayanan ka na tsarin Nisal..

Ziyarar Mallam Dr. Dikko Umar Radda ga Bankin Raya Africa