Questions And Answer About NIN

Tambaya da Amsa game da NIN.

1.Tambaya:Minene NIN?
Amsa:NIN:-National nitification number, wacce a Hausa muke kira katin Zama Dan Kasa. Wasu numbers ne da kowa ke mallaka,domin Tabbatar da cewa shi Dan Kasa ne.

2.Tambaya: a Ina ake yinta?
Amsa: mafi akasari ana yinta ne a Local government.

3.Tambaya:Da gaske ne za a dakatar da layuka, ga duk Wanda bai da ita?
Amsa:Lallai hakane Kamar yadda aka ambata za a rufe duk layukan waya, wadanda basu da ita.
Haka kuma za a rufe duk layukan da akayi Register dinsu ba bisa kaida ba.


4:Minene Amfanin saka NIN a Layi?
Amsa:Tabbas yana da matukar amfani
Ga wasu daga ciki:
1.Zai dakile duk wata hanya wacce wasu ki kiranka da sunan ma'aikatan banki, idan sunyi haka za a kamasu cikin sauki.

2.Za a iya nemo masu garkuwa da mutane, ko da ko sunyi waya da wayar Wanda suka kama.

3.Akwai miyagun mutane masu buda wata harkalla, ma'ana a yanar gizo wadanda suke cutar da mutane, Yanzu a iya ganesu cikin sauki.

4.Akwai wasu mayaudara dake kiran Mutane suna shanye musu jini, su ma za a iya kamasu.

5.Akwai masu kiran Mutane da sunan ma'aikatan wani kamfanin Layi ne, Kamar su Glo, Mtn da dai Sauransu domin a tura musu kudi.
Ta wannan hanyar za a iya kamasu.

6.Akwai masu yiwa Mutane barazanar zasu aikasu lahira, ko kuma suce zasu iskoka har gida.
Ta wannan hanyar za a iya kamasu.

7.Da yawa wasu Ke shiga wasu Kungiyoyi su yaudari mutane sai su chanza Layi! Yanzu dai za a iya kamasu.

Duk wannan hasashene nawa ni Usman Mairiga, ba lallai ne ya zamo gaskiya ba.

5.Tambaya:idan nayi ban karbo ba ya kenan?
Amsa:Da Wanda ya yi bai karbo ba, da Wanda ta shi ta bace duk zasu iya
dialling dinπŸ‘‡πŸ»
*346#
Sai dai numbers din wasu sun ce min sun daina aiki.
Amma zaku iya tambayar masana akai.


6.Tambaya:Su kuma wadanda basu yi ba, ina mafita?

Amsa:sai su garzaya suje suyi nan da 30 ga wannan watan.
Duk da yake wasu sunce abin Zai kai kusan 10 weeks kafin a rufe layukan wadanda basu yi ba.

8.Tambaya:Ina da Layi amma bani nai masa Register ba, shin Zai iya saka masa NIN?
Amsa:To gaskiya munyi magana da wani masani, ya shaidamin cewa ko anyi hakan a banza ne.
Domin sunan da aka yi Register dashi daban, sunan dake kan katinka daban.
Akan haka ne basu yarda.

9.Tambaya:Zan iya amfani da NIN nayiwa layuka fiye da daya?
Amsa:Eh zaka iya haka, amma bana Tsammanin su wuce layuka Uku.

10.Tambaya: shin zan iya yin NIN a Online?
Amsa:To gaskiya abin da wuya ya yiyu, domin dole a NIN sai an dauke hotonka, da tsawonka, sai anyi amfani da hannunka, da dai sauransu.
Wadannan dalilan zasu iya hanawa.

11.Tambaya:Kenan yanzu zan iya rike numbers din NIN da kyau?
Amsa:Eh lallai kam, ai ya zama kamar wajibi yanzu.
Kuma kada wani ya kiraka yace ka gayamaisu, domin za a iya cutarka ta wannan gefen.

12.Tambaya:Da yawan Al'umma duk suna da layukan da suka buda komai na Bank dinsu, ina mafita?
Amsa:To mafita tana ga Hukuma ko nace masana, amma a tawa fahimta akwai mafita.

Mafita ita ce:-
Shiga ka domin cigabaπŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»πŸ‘‡πŸ»
http://arewab.blogspot.combayanin-game-da-nin.html
Kar Ku manta da Turawa Yan'uwa.

Comments

Popular posts from this blog

Yadda zaka ida ceke bayanan ka na tsarin Nisal..

Ziyarar Mallam Dr. Dikko Umar Radda ga Bankin Raya Africa

RADDIN MURIC ZUWA GA BISHOP MATHEW HASSAN KUKAH!!!