Dalilin da yasa kasashen yamma suka fi mu cigaba a bangaran fasaha...

Idan ka kwantar da ranka kayi tunani da kyau za ka fahimci cewa akwai wasu dalilai da yasa kimiyya da fasaha suka ci gaba a duniya musamman a ƙasashen yamma. Sai dai dalilan a bayyane suke kuma kusan kowa ya san su, abun nunawa guda a nan shi ne “menene madogarar cigaban bunƙasa ilimi da binciken kimiyya da fasaha” bayan kuma mutane ne masanansu.

A yau duniyar kimiyya da fasaha sun yi ci-gaban da ya haura gaban mamaki domin wasu abubuwan da za ka ji ana samarwa da binciken da ake yi wajen gano wani abu dole sai dai kayi shiru don mamaki.

Amma menene dalilin haka?

A takaice kuma dalili guda daya shine “bincike.” Da bincike ake juya duniya, da shi ake canja duniya kuma da shi ake bunkasa komai.

Shekaru dari da suka wuce a baya babu ilimin yanar gizo, yau ga shi ta dalilinsa ka kan iya ganin mutumin da yake wata nahiyar kai tsaye, kawai taba jikinsa ne ba za ka iya ba. Shekaru dubu da suka wuce kafin ka kai wata kasa sai ka shafe tafiyar watanni, a yau za ka iya daga murya kayi magana kowa ya ji ka a fadin duniya; wannan shine manufar bature “making the world a global village” – saboda a ƙaramin kauye ne ko ihu kayi kowa sai ya ji.

A takaice, wato bincike a yau yayi sanadiyyar samuwar komai kuma yayi sanadiyyar gano wasu abubuwan da da Ɗan-Adam bai isa ya gano su ba.

Amma wane irin bincike tukunna?

Bincike ya rabu kashi-kashi kamar yadda masana suka kasabta, sai dai a takaicen-takaicewa za mu iya raba shi kasha biyu kacal:

  1. Binciken Kimiyya – wato a nan bincike ne ake yi domin gano wani abu. Misali ƙirƙirar wata mawarwarar sarƙaƙiyar lissafi daga tunani, gina nazariyya, fahimtar ko gano sabon wani abu da sauransu. Wannan ya jingina ne ga masana kimiyya da fasaha da duk wasu muƙarrabansu. A wannan bincike yau duniya ta ci gaba. Da wannan bincike aka iya samun ababen tafiye-tafiye, na’urori, aikin likitanci da sauransu. Irin wannan ilimin bincike shi ne wanda turawa suka duƙufa akai har suka zarcewa duniya.
    Amma me kake buƙata wajen yin irin wannan bincike?
    Lokaci, dama, tunani, karatu… shikenan!
  2. Binciken Nazari – wannan kuma bincike ne da ya shafi wurare da dama kamar binciken gano adadin yawan al’ummar Nigeria ko duniya, binciken gano wane irin taimako talaka yake buƙata, binciken gano yadda za a taimaki al’umma da cigaban su da dai sauransu. Irin wannan bincike masana harkokin siyasa, albarkatun ƙasa, falsafa, ƙididdiga, zamantakewa da sauransu suke yi. Kafin ka kai ga irin wannan bincike kana buƙatar karantar yadda lamarin yake da kuma yadda abubuwa zasu kasance

Comments

Popular posts from this blog

Yadda zaka ida ceke bayanan ka na tsarin Nisal..

Ziyarar Mallam Dr. Dikko Umar Radda ga Bankin Raya Africa

RADDIN MURIC ZUWA GA BISHOP MATHEW HASSAN KUKAH!!!