Alhamdulillah! Barka da zuwa wannnan shafi namu mai albarka muna fatan kuna jin dadin kasancewa damu a koda yaushe..
Allah ya taimaka mamu baki daya, Ameen.
Juma'at Mubarak
Get link
Facebook
Twitter
Pinterest
Email
Other Apps
-
Oh' Allah We Ask With Your Beautiful Names To Apologize Our Sins And Bless Our Life Time In This Beautiful Day, Juma'at.
Jaridar "ALIB Hausa" ta na sanar da duk wadanda ke bukatar cike Nirsal Covid19 loan da kuma wadanda su ka cika kuma cewar za su iya duba wa ko da baka sami Wani sako/sms ko kiran su ba domin ganin tabbacin matsayinka. Kuma ga misalin yadda ake dubawa kamar haka: 1) kawi ka je wannan shafin nasu http://covid19.nmfb.com.ng amma fa ba space a tsakanin rubutun. 2) sannan idan shafin ya bude, ka duba daga kasa za ka ga zabi guda 2, na farko SME na biyu Household, sai ka danna loan din da ka cike, yawancin mutane Household su ka cike a matsayin zabinsu. 3) kuma ka na dannawa, shafin zai kai ka inda za ka sa BVN number naka ka yi checking. Sannan kuma: 1) inkuma ba ka dade da yin application ba, to za ka ga 'BVN' does not exist' domin sai BVN na wanda su ka yi aiki akan shi ake dorawa a wurin. 2) ko da sun duba application naka amma ba su gama aikin ba, to za ka ga 'your application has not been approved, please check back, later'. 3) kuma idan k
Gwamnan Jihar Katsina Ya Ziyarci Bankin raya Africa, Ya nemi tallafin su kan bunkasa harkar Noma, Ilimi da Lantarki. Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, ya ziyarci Bankin Raya Afirka (AFDB) inda ya gana da Babban Daraktan Bankin, Mista Lamin Barrow a ofishin Bankin da ke Abuja a ranar Alhamis, 8 ga watan Yuni 2023. Ziyarar na da nufin tattauna batun saka hannun jari da tallafin shiga tsakanin Katsina da Bankin don taimakawa wajen bunkasa samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al’ummar jihar Katsina. Dr Radda, a cikin jawabin nasa, ya ce, "Muna bukatar taimakon Bankin musamman don magance gibin abubuwan more rayuwa na jihar, kamar wutar lantarki." Ya kuma kara da cewa, makamashin da ake sabuntawa ya kasance wani muhimmin ababen more rayuwa da ake bukata domin samun karuwar tattalin arziki a jihar, wanda hakan ya sanya ziyarar ta zama wajibi. Gwamnan ya kuma bukaci Bankin ya ba da goyon baya don bunkasa muhimman amfanin gona, da suka hada da auduga da ayyukan
RADDIN MURIC ZUWA GA BISHOP MATHEW HASSAN KUKAH SAKO ZUWAGA BISHOP KUKAH DAGA MURIC: Bishop din Diocese na Sokoto, Rev. Fr. Hasan Kukah, a maganar da yayi jiya ya ba da shawarar cewa ya kamata a yi juyin mulki da wani Dan Kudu ya mamaye kujerar mulkin Najeriya. Ya kuma ambaci Musulunci a matsayin addinin da yake kawo tashin hankali. Kungiyar kare hakkin bil adama ta musulinci ta Najeriya, kungiyar Rajin kare hakkin Musulmi (MURIC), ta bayyana bishop din a matsayin mai muguwar dabi’ar ci da ceto Kuma mai kawo hargitsi. Wannan an bayyana wa manema labarai ne a wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, 27 ga watan Disamba, 2020 ta hannun Farfesa Ishaq Akintola, daraktan kungiyar. Mun yi matukar mamakin wannan ta hanyar kai hare-haren da aka fara jiya wanda Rev. Hasan Kukah ya kaddamar kan Musulunci saboda tsana ta addini. Bishop din Katolika na Diocese na Sakkwato ya ambaci Musulunci a matsayin addini tashina-tashina. Ya kuma yi kira da a yi juyin mulki ga zababbiyar gwamnatin Shugaba Mu
Comments